14 Janairu 2020 - 09:52
Rauhani Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Maida Pentagon Hukumar Yan Ta'adda

Shugaban Kasar Iran Hassan Rauhani ya4 rattaba hannu kan wata doka da ta maida Pentagon hukumar yan ta'adda

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24-ta rawaito cewa; Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya rattaba hannu kan dokar da majalisar dokokin kasar ta yi wa gyara, wacce kuma ta fadada dokar wacce aka samar da ita a cikin watan Afrilun shekarar da ta gabata, don ta game dukkan sojojin Amurka a duniya, a matsayin hukumar yan ta’adda.
Kafin haka dai gwamnatin Amurka da sanya IRGC a matsayin kungiyar yan ta’adda a shekarar da ta gabata, sai Iran kuma ta kafa dokar maida sojojin Amurka a yankin gabas ta tsakiya wato United States Central Command (CENTCOM) a matsayin yan ta’adda sannan bayan kisan Janar Sulaimani majalisar dokokin kasar ta fadada ta zuwa kan dukkan sojojin Amurka.